(ABNA24.com) Dakarun sa kai na kasar Iraki da aka fi sani da Hashd al-Sha’abi sun sanar da harbo wani jirgin sama mara matuki na leken asiri da ke aikin leken asiri a sararin samaniyyar birnin Bagadaza, babban birnin kasar Irakin.
Dakarun sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka ce an harbo jirgin saman leken asiri mara matukin ne a lokacin da yake gudanar da ayyukan leken asiri a sararin samaniyyar birnin na Bagadaza a yammacin jiya Alhamis.
Harbo wannan jirgin leken asiri mara matuki wanda har ya zuwa yanzu ba a tantance na wata kasa ba ne ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kiran gwamnati firayi minista Adel Abdul Mahdi na Iraki da ta dau matakan da suka dace wajen kare mutumci da ikon kasa biyo bayan wani hari da aka kai sansanin dakarun Hashd al-Sha’abi din a kwanakin baya.
Da dama dai suna garin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila ne suka kai wadannan hare-hare da aka kai sansanonin dakarun na Hashd al-Sha’abin a kwanakin baya.
/129