(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran Muhamad Jawad Zarif wanda ya bayyana hakan ya kara da cewa;A lokacin da na zama ministan harkokin waje na yi rubutu a jaridar “Sharq Ausat” da a ciki na bayyana cewa; A shirye muke mu bude tattaunawa, domin tattaunawa za ta amfani wannan yankin ne da kasashen da suke cikinsa.”
Zarif ya kara da cewa; Killace wata kasa guda daya da kasashen larabawa na yankin tekun pasha su ka yi, ba abu ne wanda ya dace ba, don haka wajibi ne mu karfafa tattaunawa a cikin wannan yankin.
Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya kore labarin da ake yawo da shi na cewa; Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya tuntubi Iran domin bude tattaunawa.
Zarif ya kara da cewa; A lokacin da Saudiyya ta fara kai wa kasar Yemen hari,ta tsammaci cewa za ta iya mamaye kasar cikin kankanen lokacin, sai dai mun yi imani da cewa; Ba abu ne mai yiyuwa ba a iya samun galaba akan al’umma guda.
/129
6 Agusta 2019 - 07:13
Lambar labari: 967305
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran Muhamad Jawad Zarif wanda ya bayyana hakan ya kara da cewa;A lokacin da na zama ministan harkokin waje na yi rubutu a jaridar “Sharq Ausat”...