30 Yuli 2019 - 06:30
​Shugaban Hukumar Da ke Kula Da Hukumomin Leken Asiri Ta Amurka Ya Yi Murabus

Babban daraktan hukumar da ke kula da dukkanin hukumomin leken asiri akasar Amurka Dan Coats ya yi murabus daga kan mukaminsa.

(ABNA24.com) Tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, Dan Coats ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa, na babban daraktan hukumar da ke kula da dukkanin hukumomin lkeken asiri ta kasar Amurka ne, bayan da ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda Trump ke tafiyar da wasu ayyukansa.

Dan Coats dai ya karbi shugabancin hukumar ne tun a cikin watan Maris na shekara ta 2017, amma sun yi ta samun banbamcin ra’ayi da Trump a kan batutuwa da dama, daga ciki har da batun Rasha, da kuma Koriya ta arewa.

Dangane da batun yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya kuwa, yana ganin cewa Trump ya tafka babban kure saboda ficewar da ya yi daga wannan yarjejeniya, sakamakon yadda hakan ya zubar da kimar Amurka a duniya har ma a idon wasu kasashen turai, ganin cewa Iran tana yin aiki da yarjejeniyar, amma Amurka ce ta saba wa abin da ta rattaba hannu akansa.

Haka nan kuma yana zargin Trump da rashin iya aiki, da rashin sanin siyasa, kamar yadda kuma yake zargin Donald Trump da yawan shirga karya.



/129