23 Yuli 2019 - 04:15
Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa, Yukiya Amano ya rasu

Kamfanin dillancin labarun Sputnik ya ambato majiyar hukumar makamashin nukiliyar ta kasa da kasa yana tabbatar da mutuwar shugabanta dan asalin kasar japan.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labarun Sputnik ya ambato majiyar hukumar makamashin nukiliyar ta kasa da kasa yana tabbatar da mutuwar shugabanta dan asalin kasar japan.

A kwanakin bayan, an bayar da labarin da ke cewa; Yana da niyyar yin murabus saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Amano ya zama shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ne a 2009. Ya rasu yana dan shekaru 72.



/129