12 Agusta 2018 - 17:50
Zarif: Babu Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zareef ya bayyana cewa babu wata tattaunawa da aka shirya tsakanin Iran da Amurka a taron babban zauren majalisar dinkin duniya na shekara shekara a birnin New York a cikin watan Satumba mai zuwa.

Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto zareef yana karyata labaran da suke yaduwa a wasu kafafen yada labarai kan cewa jami'an gwamnatin kasar Iran zasu gana da tokororinsu na Amurka a taron shekare shekara na majalisar dinkin duniya a birnin New York.

A ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a shirye yake ya gana da jami'an gwamnatin kasar Iran a duyk sanda suka bukaci hakan, ya kuma bayyana cewa babu wani sharadi na ganarwar idan sun amince.

Kafin haka dai Ministan ya bayyana a jiya Asabar kan cewa kasar Iran ta rika ta dauki matsayin dangane da bukatar shugaban Trump na tattaunawa.