Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce hakika tsohon Gwamna Sanata Rabi'u musa Kwankwaso ya taimake shi a tsawon shekarun da suka kwashe suna siyasa tare.
Ganduje ya shaida hakane a wata ganawa da yayi da kafafen yada labarai, yace sun shafe fiye da shekaru 20 suna tafiyar siyasa tare da tsohon mai gidan nasa.
Manyan 'yan siyasar na Kano ba sa ga-maciji da juna tun bayan zaben shekarar 2015,
Bangaren Kwankwasiyya dai na zargin Ganduje da cin amanarsu, ta hanyar yimasa bita da kulli bayan barinsa kujerar ta gwamna.
Sai dai Gwamna Ganduje ya ce "a ganinmu ba a ci amanarsa ba sai idan shi ne bai fahimci abin da ake nufi da cin amana ba."
Ya kara da cewa; "idan kuma ya dauka cewa ya taimake ni na zama gwamnan jihar Kano ne amma kuma naki bin dukkannin manufofin sa shi yake nufi da cin amana, to mu ba ma kallonsa a matsayin shi ne cin amana."
Da aka tambayi Ganduje kan dalilin da ya sa ya kori 'yan Kwankwasiyya daga cikin gwamnatinsa, sai ya ce, "na yi watsi da su ne saboda yadda suka dinga yi wa gwamnati na zagon-kasa."
yaci gaba da cewa "babu gwamnan da zai yarda ana ma sa zagon kasa a gwamnati, ko shi Kwankwason ba zai yarda da haka ba."
"A ganinsu ba Allah ne yake ba da mulki ba, goyon bayansu ne, kuma ni a zaune kawai nake aka dauko ni aka ba ni, amma ni ma gogaggen dan siyasa ne," a cewar gwamnan, wanda ke
shirin neman wa'adi na biyu.
Gandujen yace idan har sulhunsu da mai gidan nasa bai yiyuba to yana ganin shine fa
kashin bayan jar hula'
ya ce babu yadda za a yi mutum ya haifi da, "daga baya kuma ya dawo ya ce zai dauki wuka ya yanka dan."
Rikicin Ganduje da Kwankwaso ya raba Jam'iyyar APC gida biyu a Kano, tsakanin bangaren da ke ganin yana takama da karfin gwamnati da kuma bangaren da ke ikirarin rinjayen goyon bayan jama'a.
Ganduje da magoya bayansa sun dage cewa babu wata illa da wannan rikici zai yi ga nasarar jam'iyyar a zabe mai zuwa, kuma za su iya lashe zabensu ba tare da wata matsala ba.
Sai dai wadansu masana na ganin akwai sake, inda suke cewa jam'iyyar APC za ta iya fuskantar babbar matsala matukar bangarorin biyu ba su shawo kan matsalolinsu ba.
Akwai alamar Rikicin tsohon Gwamnan Kano injiniya Rabi'u musa Kwankwaso da Gwamnan kano Dr. Abdullahi umar Ganduje zai kawo kars
16 Mayu 2018 - 16:35
News ID: 893685

Akwai alamar Rikicin tsohon Gwamnan Kano injiniya Rabi'u musa Kwankwaso da Gwamnan kano Dr. Abdullahi umar Ganduje zai kawo karshe: Daga Aliyu Muhammad,kaduna