25 Mayu 2025 - 08:07
Source: ABNA24
IRGC: Hannayenmu Na Kan Kunamar Makamanmu Cikin Shirin Maida Martani

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran: Hannnayenmu na kan kunama kuma a shirye muke mu mayar da martani da karfi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa na Ahlulbayt (As) –ABNA- ya habarta cewa: Dakarun juyin juya halin Musulunci a cikin wata sanarwa da suka fitar sun tabbatar da cewa "suna ci gaba da inganta cikakken shirye-shiryensu a fagen daga don tunkarar makiya a kowace rana," tare da yin nuni da cewa " Yatsunsu na kan kunama tare da shirin mayar da martani mai tsauri, da kakkausan martani, sama da yadda ake tsammanin za a yi ga duk wani mataki na wuce gona da iri".

Dakarun juyin juya halin Musulunci sun kara da cewa martanin "ba wai kawai zai nutsar da masu ta’addanci cikin nadama ba ne, har ma zai canja daidaiton ma'auni karfi da mulki don nuna goyon baya ga gaskiya da kuma adawa da babban Shaidan mai girma da mai wakiltarsa na sahyoniyawan a yammacin Asiya".

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi gargadi a kan "duk wata kasada da gwamnatin sahyoniyawan za ta iya dauka," yana mai jaddada cewa kasarsa za ta mayar da martani mai tsauri kan duk wata barazana ko kuma wani yunkuri na haramtacciyar hanya da za a kai mata.

Your Comment

You are replying to: .
captcha