Wani rubutaccen jawabi da kakakin sa Uche Anichukwu ya sa wa hannu, ya ce Ekweramadu ya yi karin hasken a wurin taron Majalisar Kasashen Rainon Ingila na 74, reshen Afrika, wanda gwamnan Bayelsa Seriake Dickson ya dauki nauyin shiryawa a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
Ya ce bayanin da ya yi a zauren majalisa an yi masa mummunar fahimta ne, ko kuma an sauya shi da gangan don a ci masa zarafi kawai.
Ekweramadu a cikin wancan bayani da ya yi, ya ce ‘’dimokradiyya ta sakwarkwace.”
Daga nan ya ce irin yadda gwamnan Kogi ya dauki nauyin ‘yan iska abu ne mai nuni da cewa “dimokradiyya ba ta da idanu a kasar nan. Bello idan bai hankali ba, ba zai sake cin zabe a 2019 ba. Irin yadda dimokradiyyar nan ta lalace, wa ya ce sojoji ba za su iya dawowa ba? Don haka kada mu yi wasa da dimokrafiyyar nan.”
Ekweramadu ya ce ya na girmama sojoji kwarai da gaske, kuma ba zai taba neman su dawo muki ba. Ya ci gaba da cewa shi gargadi ya yi wa ‘yan siyasa, ganin cewa irinn harmagazar da aka rika yi a Jamhuriya ta Biyu ce har ta kai sojoji suka kwace muki cikin 1983
12 Maris 2018 - 17:45
News ID: 885470

Sanata Ike Ekweramadu, ya musanta maganganun da ake ta watsawa ana danganta shi da kiran sojoji su yi juyin mulki