24 Afirilu 2017 - 15:05
Sabani Tsakanin Shekau Da Al-Barnawa Yana Taimakawa Sojoji Masu Yakar Boko Haram

Gamayyar rundunar sojojin hadin guiwa na yakar boko haram a yankin tabkin chadi ta bayyana cewa sabani tsakanin bangarorin da basa ga maciji na kungiyar Boko Haram yana taimakawa aikinsu na yakar kungiyar

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto babban komandan sojojin rundunar ta Lake Chad Basin Multi-National Task Force (MNJTF) Manjo Janar Lamidi Adeosun yana fadar haka 

Adeosun ya bayyana haka ne a lokacinda yake amsa tambayoyi a taron tattaunawa wanda ma'aikatar tsaron kasar  Amurka ta shirye, ta wayan tarho.

Taron karan bayanin dai sami halattar babban komandan sojojin Amurka a nahiyar Afrika ADRICOM, General Thomas Waldhauser, komandan sojojin tarayyar Afrika AMISON Lt. General Osman Noor Soubagleh da kuma wakili na musamman ga kungiyar tarayyar Afrika Ambassador Madeira.

Labarin ya kara da cewa an dauki sautin tattaunawan ne a karamin ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Lagis na Nigeria.288