30 Maris 2017 - 19:19
 Iran Ce Kasa Mafi Aminci A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Mujallar Times da ake bugawa a kasar Amurka ta bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce kasa mafi aminci a tsakanin kasashen da suke yankin gabas ta tsakiya.

A makalar da mujallar Times ta kasar Amurka ta rubuta ta bayyana cewa: Duk da irin halin tsaka mai wuya da yankin gabas ta tsakiya ya shiga sakamakon bullar tashe-tashen hankula amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kasa mafi aminci a yankin saboda kyakkyawan jagoranci da shiryarwa daga Jagoran juyin juya halin Musuluncin kasar Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i.

Mujallar ta Times ta kara da cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ta Iran tuni ya tsinkayi irin halin siyasar da duniya zata shiga ciki musamman batun shirin makamashin nukiliyar Iran, yakin kasar Yamen da sakamakon zaben shugabancin kasar Amurka saboda zurfin hangen nesa, kuma sakamakon kwarewarsa da sanin harkokin mulki ya yi nasarar rusa duk wasu makirce -makircen da cibiyar tsaron Amurka ta Pentagon take shiryawa kan kasar ta Iran.

Har ila yau makalar ta Times ta tabo irin gagarumar nasarar da mahangar Jagoran juyin juya halin Musulunci ta Iran kan harkar tattalin arziki ta yi wajen kyautata rayuwar al'ummar Iran tare da kubutar da kasar daga matsalolin tattalin arziki da duniya ta shiga ciki.288