Mutanen biyu sun hada da BaAmurke Micheal Sharp da ‘yar asalin Sweden Zahida Catalan a yankin da ke fama ta tashe-tashen hankula.
Kakkakin gwamnatin Congo, Mista Lambert Mende, ya shaida labarin gano gawarwakin ga kafar yada labaran Faransa AFP
An dai yi garkuwa da kwararrun ne a yankin Kasai da ke tsakiyar kasar tare da wasu ‘yan asalin Congo hudu da ke rakiyarsu a wannan lokacin.
Tun a watan Augustar bara ake fama da rikici a kasai, bayan zargin dakarun gwamnati da kashe wani jagoran ‘yan tawaye mai suna Kamwina Nsapu, da ya dadde yana adawa da shugaba Joseph Kabila.
Rikicin ya ci gaba da yaduwa har zuwa wasu yankunan kasar tare da sanadi mutuwar mutane akalla 400.