Bayan wafatin babban marja'in shi'a Ayatullah Burujardi, Imam khumain ya zama daya daga cikin marja'ian Hauzar Qum da Iran. Kuma ta hanyar daliban da su ke zagaye da shi masu kwazo da jarunta irin su Hashimi Rafsanjani ya rika wayar da kan al'ummar Iran akan manufar sauye-sauyen da tsarin sarauta ya ke son samarwa da su ne maida al'ummar kasar turawa a al'adance.
Bayanai da jawaban da Imam Khumain ya rika yi a wancan tsakanin sun rika girgiza tsarin sarauta na Pahalwi. An rika kama da musgunawa masu gwagwarmayar siyasa a wancan lokacin. Imam Khumaini da al'majiransa su ne wadanda tsarin sarautar ya sanya agaba wajen matsin lamba akansu.
A shekarar 1963, jami'an tsaro sun kai hari akan cibiyar addinin musulunci ta Hauza mafi girma a Iran, wato Faiziyya. An kashe dalibai da dama da kuma jikkata wasu haka nan kuma kame wasu. Daga cikin daliban da aka kama din da akwai Hashimi Rafsanjani. Kuma a bisa doka a wancan lokacin, daliban makarantun addini an dauke musu yin aikin soja wanda ya ke wajibi akan dukkanin dan kasa. Amma saboda gwamnatin Sha tana son korar matasa da samari daga shiga makarantun addini, ta sanya yin aiki soja a matsayin wajibi ga dukkanin dalibai. Hashimi Rafsanjani yana daga cikin daliban makarantun addini da su ka fara zuwa aikin soja.
Bayan abinda a ranar 15 ga watan Khurdad da jami'an tsaro su ka kashe mutane da duka jikkata wasu, yunkuri Imam khumaini ya fara.
Hashimi Rafsanjani wanda ya sami hutu daga aikin soja, bai sake komawa ba guje masa. Ya yi watanni yana rayuwa a boye a mahaifarsa. A wannan tsakanin ne ya fassara littadin Akram Za'aitar akan Palasdinu da rawar da 'yan mulkin mallaka su ke takawa akanta.
Gabatarwar littafin da ya rubuta tana nufin bijirewa tsarin sarauta na cikin gida da kuma na waje. Haka nan kuma bayyana mummunan halin da al'ummar Palasdinu su ke ciki.
Shakka babu, wannan littafin ya yi gagarumin tasiri akan tunanin 'yan gwgawarmaya.
Bayan da aka tilastawa Imam Khumaini yin hijira zuwa Turkiya daga can kuma kasar Iraki, a watan Nuwamba na 1964, Hashimi Rafsanjani da sauran daliban da su ka kasance a tare da Imam khumaini masu gwgawarmaya, sun zama wadanda mahukunta su ke kai wa bara da farauta.
Jami'an tsaro na Savak, wadanda su ka shahara da ban tsoro da azabtarsa sun sha kamashi a wannan tsakanin. Sai dai duk da haka, ba su iya samar da wani rauni a tsakanin wadanda su ke zagaye da Imam Khumain ba yan gwagwarmaya.
Kuma Hashimi Rafsanjani bai yi rauni ba a tsawon zamansa na kurkuku. Duk wata dama da ya samu, yana yin rubutu. A gidan kurkuku wannan damar ta samu a gare shi kuma yayi amfani da ita. A nan gaba, muna dauke da shiri mai cin gashin kansa akan rubuce-rubucen da Hashimi Rafsanjani ya yi.
A wajen kurkuku, baya ga karatu da gwagwarmaya, Hashimi Rafasanjani ya kasance mai taimakawa iyalan fursunonin siyasa da kudi.
Hashimi Rafsanjani ya kasance daya daga cikin fuskoki mafi yin fice na gwagwarmaya da tsarin sarauta na sha. Kuma a tsawon rayuwar Imam khumaini a gudun hijira a Iraki Paris, yana da alaka da shi ta kut da kuma. Kuma a lokacin da Imam Ya kafa kwamitin juyin juya hali, sunan Hashimi Rafsanjani yana ciki.
Bayan ga rawar da ya taka a tsawon gwagwarmaya har zuwa ga cin nasararsa, bayan nasarar juyin musulunci Ayatullah Hashimi Rafasanjani yana cikin wadanda suna reni jaririn juyin har ya kai ga kasaita da girma.
Duk wani ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu, da akwai hannunsa a ciki. Kuma shi ne mai daidaita bangarori daban-daban na siyasa wanda ya ke a tsakiya.