Rahotanni daga helkwatar MDD da ke birnin New York sun bayyana cewar a yau Talata ce dai kasashen Rasha da Chinan suka hau kujerar nakin kan wannan kudurin da kasashen Birtaniyya, Faransa da Amurka suka gabatar da shi bayan da kasashen Rasha, China Da Bolivia suka ki amincewa da kudurin sannan kasashen Kazakhstan, Ethiopia da Masar suka kaurace wa kada kuri'ar, alhali wasu kasashe 9 kuma suka amince da shi.
Shi dai wannan kudurin ya kumshi yin Allah wadai da kuma bakanta sunan wasu 'yan kasar Siriyan su 11 mafiya yawansu kwamandojin sojoji da kuma wasu mutane da cibiyoyi 10 na kasar da suke zargi da hannu cikin wani harin da aka kai da makami mai guba a kasar a shekara ta 2014 da 2015 lamarin da tun a wancan lokacin gwamnatin Siriya ta musanta sannan kuma kasashen Rasha da Chinan suka ce gwamnatocin Turai din ba su yi adalci ba cikin binciken na su inda suka nuna son kai ba tare da zargin 'yan adawar kasar wanda a lokuta da dama sun sha bayyana cewar sun yi amfani da irin wadannan makamai masu guban.
Wannan dai shi ne karo na bakwai da kasar Rasha ta hau kujerar naki kan kudururrukan da kasashen Turan suka shirya kan kasar Siriya, alhali ita kuma kasar China wannan shi ne na shida.288