Ma'abota Littafi
Yahudawa suna da dokoki da ba su dace da kimar mace ba, idan mun duba zamu ga suna da dokar cewar idan da namiji ya auri yarinya sai ya yi da’awar ya same ta ba budurwa ba kuma babanta bai yarda ba to baban yana iya kai jini a kyalle kotu ya ce: An yi wa ‘yarsa kazafi, idan ya ci galaba sai a ci mijin tarar azurfa dari kuma bai isa ya sake ta ba har abada, amma idan aka tabbatar da haka to ita kam za a kai ta bayan gari ne a jefe ta har mutuwa. Yaya aka san cewa zina ta yi?. Ko kuwa babu wata hanyar zubewar budurci sai ta zina?!.
Idan mutum ya saki matarsa sai ta auri wani shi ma ya sake ta to na farkon ba shi da ikon sake aurenta domin an najasta ta[1]!. Don me ya sa mace ce kawai ta zama najasa ban da shi namijin?!.
Idan dan’uwa ya zauna da dan’uwansa a gida daya sai shi mijin ya mutu ya bar matarsa to ya zama dole kan dan’uwansa ya aure ta. Idan kuwa ya ki, sai ta kama hannunsa ta kai shi gaban dattijan gari ko yanki ta cire takalminsa ta tofa masa yawu a fuska, sannan a rika kiransa da sunan: Mai tubabben takalma!. Tambaya a nan idan ba ta son sa fa? Shin ya zama dole ke nan ta aure shi?!.
Game da gado kuwa matukar uba yana da da namiji to mace ba ta da komai!. A nan ina batun hakkin mata ke nan?. Don me ya sa ba su da komai?!.
Amma game da dokarsu babu wani adadin matan da aka iyakance za a iya aura[2]!. Ke nan babu mai bakin sukan Musulunci da ya iyakance su da hudu kawai?![3].
Idan muka duba Kiristanci kuwa zamu ga babu wani bambanci sosai a mafi yawan dokoki tsakanin Kiristanci da Yahudanci, misali game da hukuncin lullubi da hijabi wanda akwai shi a Yahudanci da Kiristanci amma sai suka sassauta hukuncinsa, wanda a farkon Kiristanci rashin sanya shi laifi ne kuma aibi ne mai girma da saba doka. Duba ka ga abin da ya zo a Risalar Bulus zuwa ga mutanen Korentis da umarnin a aske gashin duk wata mata da ba ta da hijabi (lullubi) don ta ladabtu![4]. Hakan nan suka sassauta shi saboda faruwar juyin juya halin masana’antu a kasashen turai da sunan saukaka aiki ga mace don ta ji dadin yin aiki a gona da ma’aikatu, sai abin ya yi yawa har coci ta yi muwafaka da shi. Tambaya a nan don me coci ta yi shiru kan takura mata masu lullubi da ake yi a yammancin duniya da hana su wasu hakkoki har da na ilimi?!.
A nan ya kamata mutane su yi hukunci tsakanin irin wadannan dokoki da na musulunci, kuma su kwatanta su ga ni’imar da Allah ya tanada a cikin addinin musulunci da kamalarsa, da kula da hakkin mata da ba a taba samunsa irinsa ba a tarihin rayuwar dan'adam[5].
Yammacin Duniya
Amma mace a yammacin duniya muna iya cewa: Yammacin duniya sun kwaikwayi musulunci ne amma sai suka dauki wanda ya yi musu da zai taimaka musu a duniyance suka cakuda shi da al’adunsu, wato sun dauki samfur ne amma suka ki yin aiki da duk abin da ya kunsa. Koda yake a wasu mahangai nasu da yawa sun sha bamban dari bisa dari da musulunci, domin shi ya tsakaita dokokinsa ne a komai, ya kuma dora shi bisa maslaha da hadafin halittar dan'adam ne, amma su sun dauki mutum a matsayin shi ne ma’auni saboda haka sai ya zama tamkar shi ne Ubangijin kasa wanda komai ya so shi ne daidai don haka ba a hana shi cimma abin da ya sa gaba.
Yamma da suke ganin cewa sun daidaita mace da namiji a komai a nazarinsu da mahangarsu amma sai muka ga sabanin haka a aikace[6] domin har yanzu ba a samu wata mahanga ba mai iya yiwuwa a aikace in ban da mahangar musulunci. Sannan ga take hakkin mata ta yadda hatta da ma dankwali da mayafi da zata sanya a kanta da ganin damarta amma hakan yana iya haramta mata shiga ajin karatu don yin ilimi har abada. Abin mamaki yayin da namiji ya kan shake wuyansa da nektayel yana sanye da dogon wandonsa da ya rife shi gaba daya, amma mace idan ta yi hakan ta lullube jikinta gaba daya wannan abin yaka ne a wajansu.
A yamma da ake da'awar an daidaita mace da namiji a hakkin komai ba tare da la’akari da dabi’ar kowanne da Allah ya halicce shi a kan ta ba[7], sai ga shi a aikace ya nuna sabanin haka ko ma ba za a iya aikata shi a aikace ba. Yau shekara fiye da dari biyu da kafa kasar Amurka amma mutum nawa ne mace ta rike shugaban kasa, mataimakinsa, shugaban majalisa, ministan shari’a, kai ko da na harkokin waje nawa ne, da wasu mukamai da dama da ka kan iya kwatantawa? Haka ma a aikin soja mata nawa ne kuma maza nawa ne? Da yawa mun ga mata sun zama kayan talla abin biyan bukatar sha’awar maza a irin wadannan kasashe[8].
A taron Faransa ne fa a shekarar 586 bayan kaikawo da sabani mai tsanani an tabbatar da cewa mace mutum ce sai dai an halicce ta ne domin ta yi hidima ga namiji. A Ingila kuwa nan da shekaru dari baya ba a lissafa ta a cikin kidayar al’umma[9].
Mahangar Musulunci
Mahangar musulunci ta girgiza duniya a wancan zamani da ta shelanta cewa babu bambanci tsakanin mace da namiji sai da tsoron Allah a daidai wannan lokaci a duk fadin duniya daga gabas har yamma babu inda mace take da wata kima ko wani hakki muhimmi a cikin al’ummarta. Haka nan ya zo a Kur’ani mai girma fadin Allah madaukaki: “Ya ku mutane! mu mun halicce ku maza da mata… mafi girmanku a wajan Allah shi ne mafi tsoronku gare shi... ”. [10]Sannan sai ya nuna wani jagoranci da maza suke da shi a kan gida domin kowace tafiya tana bukatar jagora. Allah madaukaki yana cewa: "Lallai su mata suna da kwatankwacin abin da ke kansu na hakkoki, da kyautatawa, kuma maza suna da wata daraja a kan mata"[11].
Sai dai domin gudun ka da namiji jagoran gida ya dauka yana da ikon mamaye komai, sai Allah mabuwayi ya yi nuni da cewa Allah ya sanya muku baiwa da ya yi wa kowanne, a wani fagen mata sun fi daukaka, a wani fagen kuwa maza ne suka fi daukaka, don haka ka da namiji ya yi burin samun wasu darajoji na mata don ba zai iya samu ba, haka ma mace ka da ta yi burin samun wasu darajoji na maza don ba zata samu ba. Wanda ya mamaye halittunsa da rahamarsa yana cewa: "Kuma kada ku yi burin abin da Allah ya fifita sashinku da shi a kan sashi, mazaje suna da rabo da sakamako na daga abin da suka aikata, suma mata suna da rabo da sakamakon abin da suka aikata. Ku dai ku roki Allah daga falalarsa"[12] (maimakon burin abinda ya fifita sashinku da shi a kan sashi).
Mace da namiji a musulunci duk daya ne sai dai a aiyuka da Allah ya bambanta su daidai gwargwadon yadda halittarsu take, amma ta bangaren ruhinsu babu bambanci tsakanin mace da namiji, bambancin ya shafi bangaren jiki ne. Haka nan musulunci ya duba maslaha a cikin dokokinsa; misali a hukuncin gado musulunci ya kiyaye masalahar duka ne domin dukiyar miji tana komawa ga matarsa da ‘ya’yansa ne, amma ta mace ta kebanta da ita ne. Kuma bai wajabta mata yaki ba sai ya wajabta shi a kan namiji, haka nan ciyarwa tana kan namiji ne, ita kuwa ba ta fita daga gida in ban da larura ko wani abu na wajibin fita sai da izininsa.
Matsalar da take faruwa a kasashen musulmi ta al’ada ce ba musulunci ba, misali a wasu wurare idan mace ta yi zina aibi ne da gori ga ‘ya’yanta sabanin namiji. Haka ma auren dole ba safai a kan yi wa namiji ba, amma mace da yawa ya kan faru a kanta, wannan kuwa yana komawa al’adu ne ba musulunci ba. Amma musulunci ya daidaita mace da namiji a irada, iko, mallaka, girmamawa, rike mukami, kasuwanci, ibada, aure cikin yarda[13], Ilimi, hankali, likitanci, injiniyanci, kasuwanci, tare da fahimtar juna da mijinta.
Musulunci yana kiyaye maslahar duka bangaren mata da maza a dokokinsa, misalin dokar halarcin auren mace sama da daya, da babu wannan dokar da mata sun samu kunci a cikin rayuwa kamar maza, kuma da an sami yaduwar fasadi mai yawa a kasashe. Shari’a ta sanya dokokin daidai da dabi'ar kowanne, misalin saki a bisa ka’ida ta farko yana hannun namiji ne sai dai idan da sharadi tsakaninsu na cewa tana iya sakin kanta[14], saboda mace idan ta fusata tana da saurin yanke hukunci, don maslaha sai musulunci ya sanya irin wannan abubuwa a hannun namiji. Haka ne musulunci ya gina dokokinsa bisa hikima da maslaha domin cimma hadafin gina al’umma ta gari mai iya isa zuwa kamalar da Allah ya ke so ta kai zuwa gare ta.
Musulunci shi ne addinin da ya fi kowanne tausaya wa mace a tarihin dan'adam, kuma yana ganin rayuwar iyali ba ta cika sai da wahala a wajen gida da cikin gida, don haka ne ma ya raba rayuwar gida biyu domin ya karfafi soyaiya da kaunar juna ta taimakekeniya, don haka sai ya ba wa namiji aikin wajen, ya kuma ba wa mace aikin cikin gida. Ya sanya aikin cikin gida a hannun mace, domin mace ta fi namiji iya tafiyar da al'amuran cikin gida musamman kula da yara. Ita ce ta fi cancanta da yanayin tarbiiyar yara ta fuskacin tunani da tausayi da lafiya. Yana ganin da an ba ta aikin namiji da yake wajen gida da wannan yana nufin a dora aikinta da yake cikin gida a kan namiji ke nan, don haka ne sai ya bar aikin wahala na wajen gida a kan namiji ita kuma ya ba ta aikin cikin gida[15].
Allam Saiyid Diba’diba’i yana cewa[16]: "Bambanci tsakanin 'yan'adam mace ko namiji ne ba ya fitar da wani daga cikinsu daga nau’in da suke ciki na ‘yan’adamtaka, kuma samun kamala ga kowanne daga cikinsu abu ne wanda yake mai saukin yiwuwa ga duk bangarorin biyu ta hanyar kamalar halaye, tsarkin zuciya, imani, biyaiya, neman kusanci, don haka mafi kyawun kalma a nan ita ce fadin Allah cewa: Ba na tozarta ladan aikin mai aiki daga cikinku namiji ne ko mace, sashenku daga sashe yake. Wannan al’amari ya saba da abin da ya zo cikin Attaura da take fada a cikin Sufurul Jami’a: “… sai na samu mafi daci daga mutuwa ita ce macen da take cikin daki…”.
Sukan musulunci a yammacin duniya ya taso ne saboda gafala da rufe ido game da tarihin musulunci lokacin da ya rike duniya ya wayar wa yamma da gabas kai, ya zo da tsari da babu kamarsa, da adalci da ake buga misali da shi, da tsarin rayuwa mafi kamala a tarihin dan'adam, domin tsari ne da ba a kwatanta shi ko kusa da sauran tsaruka. Ba don Yakin harin Salib (crusade) da yamma suka kai shi kan duniyar muslulmi suka samu littattafansu ba, hada da albarkacin makarantar Bagdad da Andulus, da yammacin duniya bai gano ilimi mai yawa ko wayewar ilimi ba.
Malaman da kuka samu albarkacinsu irin su “Farabi” da “Al-kindi” malamai ne mabiya alayen manzon Allah (s.a.w), haka nan mutumin da kuke wa kirari da mafassarin ilimi mai girma “Ibn sina” ya amfana daga koyarwarsu kuma musulmi ne mai biyaiya ga Ahlul-baiti (a.s), haka ma “Ibn Rushdi” bamalike babban malamin Falsafa a Andulus. Amma sai kuka dauki wanda ya amfani al’adunku a duniya kuka jefar da wanda bai yi muku ba.
Lallai Musulunci shi ne addinin da ya fi kowanne tausaya wa mace a tarihin dan Adam, kuma yana ganin rayuwar iyali ba ta cika sai da wahala a wajen gida, da kuma zama a cikin gida, sai ya raba rayuwar gida biyu domin ya karfafi soyaiya da kaunar juna ta taimakekeniya, ya ba wa namiji aikin wajen, ya kuma ba wa mace aikin cikin gida. Ya sanya aikin cikin gida a hannun mace, domin mace ta fi namiji iya tafiyar da al'amuran cikin gida musamman tarbiiyar yara da kuma kula da lafiyarsu. Ita ce ta fi cancanta da yanayin tarbiiyar yara ta fuskacin tunani da tausayi. Addinin musulunci mai hikima yana ganin da an ba ta aikin namiji da yake wajen gida da wannan yana nufin a dora aikinta da yake cikin gida a kan namiji ke nan, don haka ne sai ya bar aikin wahala na wajen gida a kan namiji ita kuma ya ba ta aikin cikin gida duk da bai hana ta yin aikin waje ba bisa sharudansa.
[1]Wannan yana nuna karyar da suka jingina wa annabi Musa (a.s) kan cewa ya kashe budurwowi da duk wata mata da namiji ya taba kusantar ta a lokacin da ya ci nasara a kan wani gari.
[2]. A kissoshin Annabawa da suke cikin Attaurar ya zo game Annabi Sulaiman (a.s) yana da mata dari bakwai da kuyangi dari uku, Dawud (a.s) yana da mata biyu, haka ma Ibrahim (a.s). Kuma matar Musa (a.s) Maryam ta yi wa Haruna (a.s) magana don Annabi Musa (a.s) ya yi mata kishiya bakar fata ‘yar Habasha kamar yadda ya zo a Littattafansu. Almizan, j 4, shafi: 89.
[3]. Almizan, j 2, shafi: 267.
[4]. Risalar Bulus: Zuwa ga mutanen Korentis.
[5]. Ubangiji madaukaki: A yau ne na kammala muku addininku gare ku, na cika muku ni’imata gare ku, na yardar muku da musulunci shi ne addini. Ma’ida: 4.
[6]Haka nan yake dangane da Dimokradiiya da ake kira na cewa, mutum shi ne yake tafiyar da mulkin kansa, kuma yake zabar abin da ya ga dama, mun ga wannan ma ya kasa aikatuwa a aikace. Da za a yi zabe a kasa sai a cikin mutane miliyan dari miliyan goma sha biyar su shiga zabe a cikin masu zaben, sai miliyan takwas su yi rinjaye a kan miliyan bakwai. Tambaya a nan ita ce; Yaya za a yi da hakkin sauran miliya shas’in da biyu, Yaya hakkin sauran wadanda ba su yarda ma da tsarin ba, Yaya kuma batun hakkin wadancan miliyoyin da ba su yarda ba da nasu kuri’un?. Amma Musulunci Akida ce kuma tsari ne da yake duk wanda yake musulmi to a bisa abin da yake cewa da imaninsa; shi ya yarda da tsarin musulunci a matsayin abin da zai mallaki rayuwarsa a duk bangarorinta na daidaiku, da al’umma, da rayuwar gidansa, kai har ma da Lahirarsa. Domin maganar ba ta tsaya a duniya ba kawai, kuma duk wanda yake cikinsa ya yi imani da tsarin da ya kunsa har a zuci.
[7]. Ra’ayin Turai shi ne; mace ta samu ci baya ne sakamakon mummunar tarbiiyar da a ka yi mata ne a tsawon shekarun duniya, da kuma ganin da ake da shi game da ita, in ba haka ba, dabi’arta daidai take da namiji. Idan haka ne ya kamata su kawo dalili a kan abin da suke cewa, ba kawai da’awa ba, mu ba mu taba ganin wata al’umma da dabi’ar halittar mazanta da matanta ya zama iri daya da ma’anar da suke fada ba. Almizan, j 2, shafi: 276 – 277.
[8]. Duba: Hukukul insan fil islam, s: 60. Da Al’mar’atul jadida, s: 18. Da Jaridar Al’ahram: bugu: 28/6/1964.
[9]. Almizan, j 4, shafi 90.
[10]. Hujurat: 13.
[11]Bakara: 288.
[12]Nisa': 32.
[13]. Shara’i’ul islam, muhakkikul hilli, fasali na biyu; fil akdi wannazari wassiga, shafi: 498.
[14]. Minhajus salihin, saiyid khu’I, mas’ala 1359, shafi: 281.
[15]. Duk da kuwa bai hana ta aikin waje ba bisa sharuda.
[16]. Almizan, j 4, shafi 90.