15 Satumba 2015 - 03:52
Mahajjatan Nigeria shida sun mutu a Makka

Hukumar aikin Hajji ta gwamnatin Najeriya ta tabbatar da mutuwar maniyyata 'yan Najeriya shida yayin hatsarin da ya auku a Harami ranar Juma'a, inda mutane 107 suka mutu.

Shugaban hukumar, Alhaji Abdullahi Mukhtar, ya shaida wa BBC cewa huɗu daga cikin maniyyatan da suka mutu 'yan jihar Gombe ne, ɗaya daga jihar Kaduna, ɗaya kuma daga jihar Katsina.

Ya kara da cewa an gano mamatan ne cikin wadanda hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwarsu da aka ajiye gawarwakinsu a asibitoci da ke birnin Makkah.

Alhaji Mukhtar ya ce sun sanar da dangin wadanda suka mutu a hatsarin.

Tuni dai hukumomin Saudiyyar suka bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike dangane da hatsarin da ya auku yayin da wata ƙugiyar ɗaga kaya mai nauyi ta faɗo a kan masallacin Harami.

Bana 'yan Najeriya 67,000 ne ake sa ran za su yi aikin Hajjin.289