Kusan dukkan bangarorin da za su halarci taron basu amince da adadin kujerun da aka ware musu ba.
Bangarorin sun hada da jam'iyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da kuma kungoyoyin mayaka masu gaba da juna.
Dangane da hakan ne al'ummar Musulmai a birnin Bangui suka yi wata zanga-zanga ta lumana domin bayyana korafinsu.
Muhammadu Jibirima ya yi karin haske kan abin da ya sa su yin zanga-zanga, "dalili shi ne an nuna wariya tun farko a bangarorin da aka ware wa kowacce kungiya, na biyu kuma ba mu amince da wakilin da gwamnati ta ce zai jagoranci Musulmai a taron ba."
Tun shekaru biyu da suka gabata dai bayan hambarar da shugaba Francoise Bozize ake ta kokarin neman hanyoyin sasanta wa da juna a kasar.ABNA