Yunkurin kasashen da ke gabacin Afirka na magance rikicin Sudan ta kudu ya ci tura tun ballewar mataiamakin shugaban kasar Riek Machar wanda aka kora daga mukaminsa.
Yanzu haka ana saran kungiyar kasashen Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Amurka da China su jagoranci wani yunkuri da ake saran zai kawo karshen tashin hankalin a kasar.
Daruruwan mutane suka mutu a Sudan ta kudu a rikicin kasar tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar.ABNA.