Mr Ban ya yi Allah-wadai da yinkurin 'yan Boko Haram na kokarin dagula zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a jihar Gombe.
A cewarsa 'yan Najeriya sun nuna jajircewa wajen fitowa kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a.
Mr Ban ya yi kira ga bangarorin da ke hammaya a zaben sun guji tashin hankali a lokacin tattara sakamako da kuma lokacin da aka sanar da sakamakon zabukan.
An ci gaba da zabe a rana ta biyu na zaben, bayan da aka fuskanci tsaikon na'urar Card Reader.ABNA