An nada kwamiti da zai yi nazarin sunayen mutanen da za a kakabawa takunkumin wadanda suka hana samar da kwanciyar hankali a kasar. Amma Gwamnatin Sudan ta kudu ta yi gargadin cewa matakin zai lalata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangaoririn da ke rikici.
Masu shiga tsakani a Tarayyar Afrika sun ba Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Reik Machar wa’adi zuwa Alhamis su cim ma yarjejeniya domin kawo karshen rikicin kasar na tsawon watanni 14 da ya lakume rayukan dubban mutane.
Cikin watan Disamban shekarar 2013, kasar Sudan ta Kudu ta shiga rikici, lokacin da fada ya barke tsakanin dakarun shugaba Salva Kiir da ‘yan tawaye masu biyayya ga abokin adawar shi Riek Machar.ABNA