17 Disamba 2014 - 12:11
Amir Abdullahiyan; Amurka bada gaske take ba wajan yakar yan Da'ish{ isil}

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa Amurka bada gaske take ba wajan yaki da yan kungiyar Da'ish, ya kara da cewa makomar siyasar kasar syria yana hannun mutanen kasar.

 

Taskar labarai ta Ahlulbait{a.s}-abna ta rawaito cewa; mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da sashen kasashe larabawa dana Afrika Hussain Amir Abdullahiyan wanda ahalin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Rasha yace; Tehran da masko sun dauki mataki daya na nuna goyan bayansu ga kasashen syria da iraki.

Mataimakin ya kara da cewa; kasarsa da masko suna aiki kafada da kafada domin taimaka ma kasashen biyu syria da iraki yajan yakar yan ta'adda da kuma kungiyar Da'ish.

Yaci gaba da cewa kasarsa ta gindaya sharudda guda hudu wadanda zasu taimaka domin warware matsalar siyasar syria wanda wadannan sharudan sunyi kama da wanda kasar ta Rasha ta shinfida.

Amir Abdullahiyan yace Amurka bada gaske take ba wajan yaki da yan kungiyar Da'ish, ya kuma kara da cewa makomar siyasar syria yana hannun mutainen kasar.

Ya kuma kara da cewa; Rasha tana nuna goyan bayanta da gaske ga syria da iraki wajan yakin da suke da yan ta'adda.

Acikin jawabansa yayi ishara da cewa bam-bamcin mahanga dake  tsakanin Iran da Turkiya a al'amuran siyasar syria za'a iya warware sune a taiburin tattaunawa.ABNA