12 Nuwamba 2014 - 15:25

Majiyoyin asibiti a birnin Bamako na kasar Mali sun tabbatar da gano kamuwa da kwayoyin cutar Ebola a jikin wani mutum, amma hakan ba shi da wata alaka da jami'in kiwon lafiyar da ya rasu sakamakon yi wa ni dan kasar Guinea mai dauke da cutar magani

 Wani likita a asibitin Bastor daya daga cikin asibitoci mafi girma a birnin Bamako ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP jiya cewa, suna jiran bayanin ne a hukumance daga ma'aikatar kiwon lafiya kafin su bayar da bayanai dalla-dalla kan lamarin.  

 

Ya kara da cewa jami'in kiwon lafiya da ya yi wa wani dan kasar Guinea magani da yake dauke da cutar Ebola, ya rasa ransa daga bisani, wanda kuma bayan gudanar da bincike, an gane cewa shi ma ya kamu da cutar ne, kuma ita ce ta yi sanadiyyar mutuwarsa.

 

Rahotanni sun ce jami'an tsaron kasar Mali sun killace asitin Bastor da ke birnin Bamako baki daya, tare da hana mutane shiga cikinta, da kuma hana wadanda ke ciki fitowa. ABNA