2 Oktoba 2014 - 10:00
Kotun Tarayya A Lagos Ta Yanke Hukuncin Shekaru 25 Ga 'Yan boko Haram 3

Kotu ta yanke hukuncin shekaru 25 ga wasu 'ya'yan kungiyar boko haram 3 A Tarayyar Najeriya. Wata babbar kotun tarayya a brinin Legas ta yanke wa wasu 'yan kungiyar Boko Haram guda uku hukuncin daurin shekaru 25 a gidan kaso tare da aiki mai tsanani. Mutanen uku da kotu ta samu da laifi, kowannensu zai shafe tsawon shekaru 25 a gidan yari saboda shiga kungiyar ta'addanci.

An gudanar da wannan shari'ah ce cikin sirri saboda bukatar kare rayukan shaidu.

A cewar rahotanni, kotu ta gabatar da hukunci ne a gaban lauyoyi wadanda suka gabatar da kara da kuma masu kare wadanda ake kara kadai.

Wannan hukunci dai na zuwa ne, bayan da gwamnatin tarayya tayi tayin yafiya ga 'yan kungiyar ta Boko Haram wadanda suka aje makamansu kuma suka zabi sulhu gami da zaman lafiya. ABNA