25 Satumba 2014 - 15:28
Shugaban Kasar Mauritaniya Ya Jaddada Batun Yaki Da Cutar Ebola A Nahiyar Afrika

Shugaban kasar Mauritaniya ya bukaci karin kokari a matakan da ake dauka a fagen yaki da annobar cutar Ebola a nahiyar Afrika.

A jawabin da ya gabatar a zaman babban taron zauren Majlisar Dinkin Duniya; Shugaban kasar Mauritaniya Muhammad Wuld Abdul-Aziz ya bayyana cewar annobar cutar Ebola hatsari ne babba da ke barazana ga dukkanin kasashen nahiyar Afrika, don haka akwai bukatar kasashen duniya su kara yunkurowa domin ganin an shawo kan matsalar cutar cikin gaggawa.

Har ila yau shugaban kasar ta Mauritaniya ya bayyana cewar kasarsa ta kara samun habaka a fagen harkar noma, don haka akwai bukatar karfafa kasuwar kayayyakin noma a Mauritaniya da nufin taimaka wa manomar kasar. ABNA