23 Satumba 2014 - 08:50

Gwamnatin kasar Saliyo ta bayyana cewar an sami gagarumar nasara a dokar hana zirga-zirga ta kwanaki uku da ta kafa a kasar don dakile yaduwar cutar Ebola wacce ta kunno kai kuma take ci gaba da kashe mutane a kasar.

A wata sanarwa da ta fitar a jiya, gwamnatin Saliyon ta ce sakamakon binciken da aka gudanar tsawon wadannan kwanaki uku an sami nasarar gano wani adadi mai yawa na mutanen da suka kamu da cutar amma suke boyewa, tana mai cewa a nan gaba za ta bayyana adadin da aka gano din bayan an gama gudanar da bincike, duk da cewa wasu majiyoyin sun ce an gano sama da mutane 150 da suke da cutar.

 

 

Kafafen watsa labaran kasar Saliyon sun ce sakamakon wannan matakin da gwamnati ta daukan hakan ya sanya wasu mutane da suka kamu da cutar bayyanar da kansu ta hanyar buga wayoyi zuwa ga kafafen watsa labarai da kuma cibiyoyin da abin ya shafa inda suka sanar da kansu a matsayin wadanda suka kamu da cutar.

 

Ita dai wannan dokar ta fara ne daga ranar Juma’ar da ta gabata zuwa lahadi, inda kimanin likitoci da malaman duba gari 30,000 suka gudanar da bincike gida-gida don gano wadanda suka kamu da cutar ta Ebola wacce ya zuwa yanzu ta kashe sama da mutane 500 a kasar. ABNA