19 Satumba 2014 - 13:01
A Jiya Alhamis An Kashe Sojojin Chadi Guda 5 A Rewacin Kasar Mali

Rahotanni daga kasar Mali sun ce sojojin kasar Chadi 5 da suke aikin wanzar da zaman lafiya a arewacin sun rasa rayukansu sakamakon tashin wata nakiya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, nakiyar ta tarwatse a lokacin da wata mota da ke dauke da sojojin na Chadi ta bi ta kanta a yankin Agiluk da ke arewain kasar a jiya Alhamis, a nan take 5 daga cikinsu suka rasa rayukansu wasu kuma suka samu ranuka.

 

A ranar 14 ga wannan wata na Satumba wani sojin kasar ta Chadi guda a wani yanki da ke kan iyakan kasar ta Mali da kuma Aljeriya, haka nan kuma a ranar 2 ga wannan wata har ila yau an kashe wasu sojojin kasar vat Chadi a arewacin kasar ta Mali, tare da jikkata wasu kimanin 15.

 

Rundunar sojin kasar Mali dai ta dora alhakin hakan a kan masu tsatsauran ra'ayi da ke dauke da makamai da suke da alaka da kungiyar alkaida. ABNA