13 Satumba 2014 - 10:14

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce yana da shiri na musamman dangane da hanyoyin da za a fuskanci cutar Ebola a kasashen yammacin nahiyar Afirka, domin kawar da kwayoyin cutar baki daya.

Kakakin fadar White House Josh Earnet ne ya bayyana hakan a jiya a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce a ranar Talata mai zuwa Barack Obama zai nufi jahar Atlanta inda zai gana da manyan jami'an kiwon lafiya na kasar Amurka, domin tattauna hanyoyin yaki da cutar ta Ebola a kasashen yammcin Afirka, da kuma rawar da Amurka za ta taka a wannan fage.

 

A wata zantawa da ta hada shugaba Obama da tashar talatabijin ta NBC news a ranar Lahadi da ta gabata ya bayyana cewa, Amurka za ta tura sojoji masu kula da kiwon zuwa kashen ta cutar da Ebola ta yi kamari, wato Guinea Conkry, Saliyo da kuma Liberia, domin bayar da agajin gaggawa ta bangaren kiwon lafiya, tare da kafa tantuna na musamman domin gudanar da ayyuka na yaki da cutar. ABNA