2 Satumba 2014 - 10:58
Kasar Saudia Ta Dakatar Da Bada Visar Shiga Ga Matafiya Daga Wasu Kasashen Yammacin Africa

Har,yanzun dangane da cutar ta Ebola, hukumomi a kasar saudia sun bada sanarwan dakatar da bada Visar shiga kasarta ga matafiya daga wasu kasashen yammacin Africa wadanda suke fama da cutar ta Ebola.

Kamfanin dillancin labaran kasar ta saudia WAS ya nakalto wani bayani daga ma’aikatar aikin kasar tana fadar haka a jiya Litinin.

Bayanin ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ta dakatar bada visar shiga kasar ga masu shigowa kasar daga kasashen Liberia, Salio da kuma Guinea.

A tarayyar Nigeria dai har yanzun maniyyata aikin hajjin bana kimani dubu 76 suna sauraron kasar saudia ta fara bada visar aikin hajji a garesu kamar yadda ta yi alkawari.

Hukumar aikin hajji a tarayyar ta Nigeria ta sanya ranar 6 ga wannan watan na satumba a matsayin ranar da za’a fara jigilar mahajjata zuwa kasar ta Saudia. Sai dai an sami jinkiri wagen bada Visar.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa matsalar na’ura ce a karamin ofishin jakadancin saudia da ke birnin Kano ya hana a fara tanatance passport na mahajjatan, kuma da zarar an warware matsalar za’a fara ba da visar.

Mutum 6 ne kacal suka rasu sanadiyyar cutar Ebola a tarayar Nigeria sannan wasu 15 ne suke jinya, sanadiyyar kamuwa da ita. ABNA