Shafin sadarwa na tashar talabijin ta RTBF ya bayyana cewa, rundunar sojin kasar Kamaru ta dauki wasu kwararan matakai a kan iyakokinta da Najeriya, bisa la'akari da barazanar da kasar take fuskanta daga mayakan kungiyar Boko Haram, inda yanzu haka aka jibge wasu sojojin kundumbala a kan iyakokin kasashen biyu, gami da tankokin yaki da kuma jiragen masu safkar angulu da suke shawagi a yankunan.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne rundunar sojin kasar Kamaru ta sanar da kashe mayakan kungiyar Boko Haram su 8 tare da kame wasu 48, a wata musayar wuta da suka yi da su a lokacin da suka shigo cikin kasar daga wasu yankuna na Jahar Borno da ke iyaka da kasar ta Kamaru.ABNA