Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Inas Alawi, marubuciyar jarida 'yar Tunisiya da ta halarci jana'izar gawar jagora shahidin juyin juya halin Musulunci, tana mai nuni ga kasancewarta a wannan taro, ta ce: Mun zo nan don halartar jana'iza ne. Jagora shahidi (Allah Ya yarda da shi) ya kasance a matsayin Madogara, uba da jagora wanda ya haɗa kishi, ƙarfin girman kwarjini a lokaci guda.
Ta kara da cewa: Mun koyi abubuwa da yawa daga gare shi, kuma mun bi tafarkinsa da na Imam Hussain (A.S). Imam Khamene'i ya ce: "Isra'ila bai kamata ta wanzu ba," "Amurka bai kamata ta wanzu ba," masu girman kai dole ne su gushe kuma Amurka bai kamata ta mallaki duniya ba. Tare da shi mun sami 'yanci kuma mun sami ikon cewa "A'a," kuma da 'yanci da kwanciyar hankali, muna bayyana ra'ayinmu.
Wannan marubuciyar jarida 'yar Tunisiya ta bayyana cewa: Sayyid Ali Khamene'i ya nisantar da mu daga wautar dogaro ga kasashen waje. Mun kasance masu dogaro da Amurka da kuma kasashen yamma waɗanda suke mallakar duniya. Mun gode wa Allah mun bi tafarkin jagoran da a dukan rayuwarsa yake fatan shahada.
Ta kuma yi nuni ga shekarun jagora shahidi a lokacin shahada, ta ce: Ya kasance a gab da shiga shekara casa'in, kuma yana tsoron ya mutu a kan gado, amma kaddara ta shahada ta kawo masa daraja da girma, kuma an yi jana'izar gawarsa da wannan girma da halarta mai yawa. Muna gode wa Allah don wannan ni'ima ta shahada.
Alawi ta jaddada cewa: Jagora shahidi ya bar mana gadon Daukaka da Mutunci. Tare da shi mun koyi cewa kada mu zama ƙasƙantattu, kuma kada mu durƙusa a gaban makiya.
Jagora Shahidi; Hussain (A.S) Na Zamaninmu
Ta kuma yi nuni ga rawar jagora shahidi wajen bayyana lamarin Karbala ga tsatson wannan zamani, ta ce: Jagora shahidi ya zana lamarin Karbala bisa ga yanayin da ake ciki yanzu. Na yi imani cewa shi ne Hussain (A.S) na zamaninmu. Lokacin da na ce shi ne Hussain na zamaninmu, burina ba wai kawai Shi'a ba ne, a'a, kowane mutum mai mutunci yana cikin wannan kewayan. Hussain (A.S) alama ce ta mutunci da ‘Yan adamtaka ba wai kawai ga Shi'a ba, a'a, ga kowa, kuma Yazid alama ce ta ƙasƙanci da rashin tsarki ba wai kawai ga Ahlus-Sunnah ba, sai dai akasin haka.
Wannan marubuciyar jarida 'yar Tunisiya a ƙarshe ta yi ishara da cewa: Imam Khamene'i ya zana lamarin Karbala a idanunmu don ya zama ba labari kawai ba ne. Abin da ke faruwa a yau, ci gaba ne da tafarkin Karbala a wannan yaƙi tsakanin gaskiya da ƙarya.
……………………
Your Comment