Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: "Hassan Hilal" yana tafiya tsakanin layukan kaburbura yana neman kabarin 'yarsa. Ya san hanyar zuwa kabarin da zuciyarsa, amma duk lokacin da ya matso kusa takun kafarsa na kara raguwa. Kamar dai ba a auna nisan wurin da mita ba, sai dai saboda zurfin raunin da ya wanzu acikinsa tun daga wannan rana.
Bisa ga rahoton shafin labarai na "Al Jazeera Net," a makabartar garin "Mifdoun" a kudancin Lebanon, babu wani abu acikinta da ya waznu kamar da. Gilashin da suka karye suna warwatse tsakanin kaburbura, duwatsu sun kau daga wurinsu sakamakon hare-haren sama na gwamnatin yahudawa, wasu kaburbura sun balle daga wurinsu sakamakon fashewar bamabaman, wasu kuma sun tsage, kamar dai suna nuna raunin masu rai. Wasu tarin ƙura kuma ya rufe wasu sunaye waɗanda ake zaton mutuwa ta kawo musu kwanciyar hankali nesa da yaƙi.
Hassan ya isa kabarin 'yarsa Narjis. Da hannunsa yana share ƙasar da ke kan kabarin a hankali, yana kawar da busasshen reshe da ya faɗo a kan dutsen, kuma ya tsaya shiru. Ba ya yin addu'a ko zubar da hawaye. Shiru, shine kawai harshen da zai iya bayyana wannan baƙin ciki.

Daren Da Komai Ya Canza
'Yan watanni kaɗan da suka gabata, Narjis 'yar shekara biyar, tare da dariyarta da tambayoyinta na yara, ta cika gidan da farin ciki. Amma a daren 2 ga Maris 2026, a daidai lokacin da gwamnatin yahudawa ta fara yaƙi a kan Lebanon, rayuwar iyalin Hassan ta canza canji na har abada.
A lokacin da aka fara hare-haren, yana wurin aikinsa. Labarin harin bama-bamai da aka yi a Beirut, kudancin Lebanon da yankin Bekaa ana buga su daya bayan daya. Da farko bai fahimci girman bala'in ba, amma wani yanayi kawai ya fara a cikinsa. Cewa babu wani abu da zai sake zama kamar da.
Kiran waya daya bayan daya ba a amsa ba. Matarsa ba ta amsa ba, maƙwabta ba su da labari, kuma kawai kalmar da ake maimaitawa ita ce ginin ya lalace.
Ya kwashe sa'o'i yana yawo tsakanin asibitoci, motocin agaji da labarai masu karo da juna har gaskiya mai ɗaci ta bayyana, Narjis ba ta nan raye.

Sabuwar Damuwa; Shin Kabarinta Ya Wanzu?
Tun daga wannan rana, hanyar zuwa makabarta ta zama wa Hassan ba ziyara ta yau da kullun ba, a'a, ci gaba da hanyar da ta ragu a ƙofar gidan da ba a karasa ba.
Amma yaƙi bai tsaya a nan ba. Lokacin da aka buga hotunan harin bama-bamai a ƙauyukan kudancin Lebanon, Hassan bai ƙara damuwa da gidansa ko shagon da ya kone ba. Wata tambaya ce kawai ke damun hankalinsa: Idan kabarin 'yata ma ya lalace fa?
Bayan tsagaita wuta, ya shiga makabarta cikin damuwa. Ya duba kaburbura daya bayan daya. Wasu sun karye, wasu sun rushe, wasu kuma da kyar suka tsira daga lalacewa gaba daya. Amma kabarin Narjis yana nan; ko da yake ba kamar da yake ba. Wannan ya isa ya hana duniyar Hassan ta sake rugujewa.

Labarin Da Ke Maimaita Kansa A Kudancin Lebanon
Makabartar garin Mifdoun ba ita kaɗai ba ce misali. A ƙauyuka da yawa na kudancin Lebanon, hare-haren sama da fashe-fashe sun lalata makabartu. Kaburbura sun karye, makabartu sun rushe, kuma tarkacen kasar ya cakuda da busassun furanni da iyalai suka bari a kaburburan 'yan uwansu a ziyararsu ta ƙarshe.
A wani yanayin da aka maimaita sau da yawa, mutane da yawa bayan sun koma ƙauyukansu a kudancin Lebanon, kafin su ziyarci gidajensu, sun je makabartu. Kamar dai tabbatar da lafiyar kaburburan 'yan uwansu ya fi muhimmanci a gare su fiye da makomar gidajensu.
A garin "Burj Qalawiyah," wata tsohuwa ta sunkuyar da kanta kan kabarin mijinta, ta ɗauki guntun dutsen marmara da ya tsage, ta share ƙura da gefen gyalenta, kuma ta mayar da shi a wurinsa a hankali. Kamar dai tana neman gafarar mijinta cewa yaƙi ya kai har kabarinsa.
A wani wuri kusa, wani mutum yana kallon kaburburan da gutsuttsuran bamabamai suka lalata wasu sunaye da aka sassaka a kansu. Ya ce matattu ba sa tsoron bama-bamai, amma masu rai suna buƙatar wuri don saduwa da 'yan uwansu da kuma kiyaye alaƙa da su.

Makabartu Ma Suna Cikin Hare-Haren Yaƙi
Sakamakon yaƙin gwamnatin yahudawa a kan Lebanon bai tsaya ga gidaje, hanyoyi da gonakin noma ba. Makabartu, waɗanda ya kamata su zama wuri na ƙarshe nesa da tashin hankali, su ma an kai musu hari a wannan yaƙi, wanda ya ƙara sabon azaba ga tunanin jama'a.
Rahotanni na shari'a da kafofin yada labarai na Lebanon sun ba da labarin lalacewar makabartu a ƙauyuka kamar "Yahmar al-Shuqif," "Deir Qanoun al-Nahr," "Burj Qalawiyah," "Shamshtar," "Nabi Sheet" da wasu yankuna da yawa a kudancin da gabashin Lebanon.
Wannan lalacewa ba ta tsaya ga ƙauyukan da ke kan iyaka a kudancin Lebanon ba, har ma ta kai ga zurfin yankunan kudancin ƙasar da Bekaa, kuma ta haɗa da makabartu da wuraren ibada.

Tambayoyin Shari'a Da Ɗabi'a
Bisa ga dokokin jin kai na kasa da kasa, makabartu, kamar wuraren ibada da wuraren al'adu, suna cikin dukiyoyin fararen hula da suke da kariya, kuma an haramta kai hari ko lalata su sai idan ana amfani da su kai tsaye ga soji.
Don haka, abin da aka rubuta a wasu daga cikin waɗannan lamuran, na iya zama abin bincike da kuma bayar da amsa ta fuskar shari'a da ɗabi'a.

Amma a fagen gaskiya, doka tana rasa launin aikinta. Abin da ya rage shi ne duwatsu a warwatse, kaburbura da suka lalace, sunaye da suka ɓace, da iyalai da ke ƙoƙarin sake gyara alaƙar da ke tsakanin rayuwa da mutuwa, ko da yake yana da wuya.
A ƙarshe, makabartu ba wuraren binne matattu kaɗai ba ne, su ne ƙananan taswirorin ƙwaƙwalwa da asalin mutane. Kuma lokacin da yaƙi ya kai gare su, ba wai kawai duwatsu suka rushe ba, a'a, amincin tsaro da kwanciyar hankali ma suna karyewa ne.
…………………………………………
Your Comment