5 Yuli 2026 - 22:16
Source: ABNA24
Shahadar Jariri A Yammacin Ramallah Bayan Mamaya Ya Hana Kai Shi Asibiti

Majiyoyin lafiya a yau Lahadi, sun tabbatar shahadar wani jariri sakamakon hanawar da sojojin mamaya don kai shi jinya ta ƙofar Deir Ammar da ke yammacin birnin Ramallah wadda aka rufe tun watanni 5 da suka gabata.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Yaron "Ahmad Ma'ruf Zaid" ya rasu bayan sojojin mamaya suka hana wucewa ta ƙofar Deir Ammar, yammacin Ramallah wadda aka rufe tun watannin baya, duk da cewa lafiyarsa tana cikin mawuyacin hali kuma tana buƙatar a kai shi cikin gaggawa don samun jinya.

Wakilinmu ya ba da rahoton mutuwar yaron Ahmad Ma'ruf Zaid (dan wata 4) sakamakon sojojin mamaya sun ki bari a wuce da shi ta ƙofar Deir Ammar inda lafiyarsa ke cikin mawuyacin hali saboda rashin lafiyar da yake fama da ita kafin ya rasu.

Kuma tun daga 8 ga Oktoba 2023, Yammacin Kogin Jordan na fuskantar tashin hankali na Isra'ila da sojojintaI da Yahudawa ke aiwatarwa, wanda ya haifar da shahadar Falasdinawa 1,175 da raunata 12,919, baya ga kama kusan 24,000 da korar 33,000, bisa ga bayanan hukumar Falasdinu.

………………

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha