Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Majalisar Lardin Babil ta Iraki ta sanar da rufe ofisoshi a wannan lardin a ranakun Laraba da Alhamis. An yanke wannan shawara a cikin shirye-shiryen gudanar da jana'izar gawar Shahid Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'i a garuruwan Iraki, kuma a lokaci guda jami'an lardin Babil sun sanar da kammala shirye-shiryen tsaro, ayyuka da kiwon lafiya na musamman don wannan taro.
"As'ad al-Muslimawi" shugaban majalisar lardin Babil Iraki a taron manema labarai bayan gudanar da taron gaggawa na wannan majalisa ya bayyana cewa: Iraki tana alfahari da kasancewa mai karbar bakuncin gawar Shahid Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'i.
Ya kara da cewa majalisar lardin Babil na Iraki, da kuri'ar mambobin, ta ayyana ranakun Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu a wannan lardin domin 'yan ƙasa su iya halartar taron jana'izar.
Keɓe Motoci 400 Don Jigilar Mahalarta
Al-Muslimawi, yana mai nuni ga kudurorin taron gaggawa na majalisar lardin Babil, ya ce wannan taron ya mayar da hankali kan manyan batutuwa biyu, wato shirin ayyuka da tsarin tsaro.
A cewarsa, an keɓe motoci 400 don jigilar mahalarta daga lardin Babil zuwa Najaf da Karbala, kuma an gudanar da hadin gwiwa mai yawa don sauƙaƙe zirga-zirga da hana cikas a harkar sufuri.
Aiwatar da Tsarin Tsaro Da Ayyuka Na Gaba Daya
Shugaban majalisar lardin Babil ya kuma ba da rahoton tsara wani cikakken tsarin tsaro tare da hadin gwiwar kwamandan 'yan sanda na Babil da 'yan sandan zirga-zirga.
An tsara wannan tsarin da nufin daidaita zirga-zirga, rage cunkoson ababen hawa, sauƙaƙe motsin masu makoki, Maukibobin Kabilu, da tabbatar da tsaron taron.
Cikakken Shirye-shiryen Hukumomin Aiwatarwa
A halin yanzu, "Ali Turki" gwamnan Babil shi ma ya sanar da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen sufuri, tsaro da kiwon lafiya, kuma za a fara aiwatar da shirye-shiryen aiki tun daga yau Lahadi.
Ya kara da cewa lardin ya tanadi motoci masu yawa don jigilar mahalarta, kuma ban da tsarin tsaro, an kuma shirya wani cikakken tsarin kiwon lafiya don wannan taro. Taron da a karon farko a wannan matakin ake gudanarwa a lardin Babil.
Kai Gawar Daga Qom Zuwa Najaf Sannan Karbala
A lokaci guda, wasu larduna da dama na Iraki su ma sun sanar da cewa za su ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu don halartar jana'izar Shahid Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'i.
Dangane da shirin da aka sanar, za a kai gawar Shahid Ayatullahil-Uzma Khamene'i bayan jana'izar a birnin Qom zuwa filin jirgin sama na kasa da kasa na Najaf, kuma bayan gudanar da tarukan ziyara da bankwana a haramin Amiril-Mu'minin (A.S), ayukan jana'izar zai isa zuwa Karbala.
Sa'an nan za a kai gawar shahidi daga titin Shahid Abu Mahdi al-Muhandis na birnin Karbala mai tsarki zuwa yankin tsakanin haramain domin a gudanar da jana'izar jama'a tare da halartar 'yan ƙasa da yawa. Bayan kammala wannan taro, za a mayar da gawar zuwa filin jirgin sama na Najaf, kuma daga nan za a kai ta don binne ta a haramin Imam Raza (A.S) a birnin Mashhad.
………………..
Your Comment