Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Majiyoyin cikin gida sun ba da rahoton yawaitar hare-haren sojojin gwamnatin yahudawa da hare-haren Yahudawa ‘yan kama wuri zauna a yankuna daban-daban na Yammacin Kogin Jordan ciki har da Al-Khalil, Ariha, Tulkarm, Nablus, Jenin da Bethlehem, inda sojojin suke yin bincike a gidaje da kama wasu 'yan Falasdinu, su kuma ‘yan kama wuri zauna suka kona gonaki, lalata motoci da kai hari a wani wurin shan kofi a kudancin Nablus.
Bisa ga wannan rahoto, yankuna a Al-Khalil, Ariha, Tulkarm, Nablus, sansanin Askar, Bethlehem da birnin Jenin sun fuskanci hare-haren mamaya. Sojojin yahudawa a waɗannan hare-haren, sun binciki gidaje da gine-gine da yawa kuma sun kama wasu.
A lokaci guda, mazauna yahudawa a arewa maso gabashin Ramallah sun kona gonakin Falasdinu, kuma a kudancin Nablus sun kai hari kan wata mota da gidan Falasdiniawa. Sun kuma kona wani wurin shan kofi a kudancin Nablus. A kudancin Al-Khalil ma, sun lalata dukiyoyin Falasdinawa.
……………………
Your Comment