5 Yuli 2026 - 16:04
Source: ABNA24
Isra’ila Ta Yaye Kallabin Hadin Gwiwar Tsaronta Da UAE A Yaƙinta Da Iran

Ministan Sufuri na gwamnatin yahudawa a karon farko a hukumance ya bayyana cewa a yayin yaƙin baya-bayan nan da Iran, Tel Aviv ta aika da wata na’urar tsarin tsaron sama "Kubbar Karfe" zuwa UAE, kuma ta tura wasu sojojinta zuwa ƙasar UAE don gudanar da wannan na’urar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Miri Regev, Ministan Sufuri na gwamnatin yahudawa, a karon farko a hukumance aa bayyana hadin gwiwar soji na wannan gwamnati da UAE a yayin yaƙin baya-bayan nan da Iran.

Ya sanar da cewa a yayin wannan yaƙi, Tel Aviv ta aika da wata na’urar harba makaman kariya na tsaron sama "Kubbar Karfe" zuwa UAE. Bisa ga rahotannin kafofin yada labaran Ibrananci, an yanke wannan shawara ne bayan tattaunawar wayar tarho tsakanin Benjamin Netanyahu, firayim ministan gwamnatin yahudawa, da Mohammed bin Zayed Al Nahyan, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, a daidai lokacin da hare-haren Iran ke ƙaruwa.

Waɗannan rahotanni sun kuma nuna cewa gwamnatin yahudawa, baya ga aika nau’rar tsaro, ta kuma tura sojojinta da dama zuwa ƙasar UAE don girke da gudanarwa ta amfani da wannan nau’ra. Bisa ga waɗannan rahotanni, waɗannan sojoji sun taka rawa wajen kakkabo wasu makamai masu linzami na ballastic da jirage mara matuki na Iran.

Waɗannan maganganun, suna nuna hadin gwiwar soji kai tsaye da ba a taɓa yin irinsa ba tsakanin gwamnatin yahudawa da UAE a yayin yaƙin baya-bayan nan da Iran.

…………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha