Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: A Jami’ar Al-Mustafa Khatamul-Nabiyyin (S.A.W) ta Jacobabad, an gudanar da wani taro na ilimi da tunawa da shahidin jagora mai taken "Manufar Karbala A Mahangar Shahidin Jagora" a ƙarƙashin jagorancin Allamah Maqsud Ali Dumaki. Wannan taron ya sumu halartar da yawa da malamai, masu wa'azi, shugabannin addini da zamantakewa da kuma wasu gungun masoya Ahlul-Bayt (a.s).
A wannan taro, Allamah Zulfiqar Ali Sa'idi shugaban lardin na Majalisar Malaman Makarantar Ahlul-Bayt (a.s), Maulana Saif Ali Dumaki mataimakin manajan Al-Mustafa Khatamal-Nabiyyin (S.A.W), Maulana Ali Nawaz Irfani mai wa'azin addini na Cibiyar Wa'azin Musulunci, Allah Bakhsh Sajjadi babban sakataren reshen matasa na Majalisar Hadin Kan Musulmin Pakistan, Maulana Munawar Hussain Solangi sakataren tsarawa na lardin na Majalisar Hadin Kan Musulmi da sauran malamai da shugabannin addini ne su kai yi jawabai.
Allamah Maqsud Ali Dumaki a cikin jawabinsa na shugabanci ya ce: Jagora mai girma shahidi Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (Allah ya jiƙansa) ya rayar da manufar Karbala da saƙon Ashura a wannan zamani. Ya gabatar da tafsirin Alƙur'ani, na ilimi da juyin juya hali na yunkurin Imam Hussain (A.S) wanda ba wai kawai al'ummar Iran ba, har ma dukan al'ummar Musulunci ya kirasu zuwa ga basira, daraja, 'yanci da tsayin daka. Ya kara da cewa jagora shahidi ya kasance koyaushe yana tsayayya ga Yazidawan zamani, masu girman kai na duniya musamman Amurka da gwamnatin yahudawa, ya taimaki waɗanda ake zalunta kuma ya nuna hanyar daraja da 'yanci ga al'ummar Musulunci.
Ya kuma bayyana cewa: A yau zukatanmu suna bugawa a Tehran; inda ake gudanar da jana'izar tarihi na jagoran gwagwarmaya kuma masoyin al'ummar Musulunci, Shahidi Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i.
Allamah Zulfiqar Ali Sa'idi ya ce: Lamarin Karbala ba wai kawai wani lamari ne na tarihi ba, a'a, ma'auni ne na dindindin na bambance gaskiya da ƙarya a kowane zamani. Jagora shahidi ya mayar da wannan tunanin Husaini a matsayin jigon farkawa na al'ummar Musulunci da hadin kan Musulmai.
Maulana Saif Ali Dumaki ya bayyana cewa: Watan Muharram yana koya mana darasi na kiyaye addini, sadaukarwa, ƙwazo da juriya a kan gaskiya, kuma jagora shahidi ya sadaukar da dukan rayuwarsa don yaɗa waɗannan dabi'un Musuluncin.
Maulana Ali Nawaz Irfani ya ce: Tunani na shahidin jagora ya samo asali ne daga Alƙur'ani mai girma, tarihin Annabi (S.A.W) da koyarwar Ahlul-Bayt (a.s), kuma ya kasance koyaushe yana kiran matasa zuwa ga ilimi, taƙawa, basira da sanin makiya.
Allah Bakhsh Sajjadi ya jaddada cewa: Aikin matasa ne su aiwatar da saƙon Ashura a rayuwarsu ta zahiri, kuma su taka rawa mai tasiri wajen haɗin kan al'ummar Musulunci, ƙarfafa Pakistan da taimakon waɗanda ake zalunta.
Maulana Munawar Hussain Solangi shi ma ya ce: Dukan rayuwar shahidin jagora yaƙi ne mai ci gaba wajen fuskantar zalunci, girman kai da yahudanci, kuma a yau ya zama dole mu isar da tunaninsa da saƙonsa ga mutane, kuma mu yi ƙoƙari tare don faɗaɗa al'adun Husaini.
A ƙarshen wannan taro, an yi addu'a don ɗaukaka darajar shahidin jagora Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (Allah ya jiƙansa), hadin kan al'ummar Musulunci, nasarar al'ummar Falasdinu, Lebanon, Iran da Pakistan da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin Pakistan.
……………………………………..
Your Comment