28 Yuni 2026 - 22:57
Source: ABNA24
IRGC Ta Lalata Matsugunai Da Cibiyoyin Ruwan Amurka

Hare-Haren Daren Jiya Sun Haifar Da Canjin Dokokin Yaƙin Inda Sojojin IRGC Suka Lalata Matsuguni Da Cibiyoyin Kula Da Ruwa Na Amurka!

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: A cewar wani ƙwararren harkokin tsaro da soji: Ƙididdiga sun nuna cewa a fafatawar da aka yi a daren jiya, Sojojin Irgc sun ɗaga dokokin yaƙi zuwa matakai da yawa.

Da safiyar yau, an lalata wurare takwas da ke da alaƙa da 'yan ta'adda gaba ɗaya, waɗanda suka haɗa da matsuguni masu mahimmanci da cunkoso, cibiyar kula da teku da sarrafa bayanai, hasumiyoyin sa ido, na'urorin radar da sadarwa a sansanin Ali Al-Salem, da kuma rundunar ta biyar (na Amurka) wadda ta kasance tana aiki a kwanakin baya-bayan nan kuma aka sake rayar da ita bayan yaƙin.

..............................

Your Comment

You are replying to: .
captcha