Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Shugabar wucin gadi ta Venezuela, Delcy Rodríguez, ta sanar da cewa sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi mai yawa da ta afku a ƙasar, akalla mutane 164 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 971 suka samu raunuka.
Batan mutane sama da dubu 21,000 sakamakon girgizar ƙasar Venezuela mai tsanani sun ɓace
Sakamakon girgizar ƙasa mai tsanani da ta afku a Venezuela, an fitar da kididdiga mai cike da damuwa game da batan 'yan ƙasar. Dangane da rahotannin farko, har zuwa yanzu an samu ɓatan mutane sama da 21,000, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin nemo su.
Biyo bayan hakan an samu saƙonni juyayi da jajantawa daga ƙasashe da dama ciki har da ƙasar Iran in da ta nuna juyayinta ga abinda ya faru da Venezuela na girgizar ƙasa mai tsanani a ƙasar
Bayan girgizar ƙasa mai tsanani da ta afku a Venezuela, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, yayin da yake nuni da jajantawar ƙasarsa ga gwamnati da al'ummar Jamhuriyar Bolivariya ta Venezuela, musamman iyalan wadanda suka rasa rayukansu, ya yi addu'ar Allah ya ba wa wadanda suka samu raunuka da wadanda abin ya shafa lafiya da waraka.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen, yayin da yake bayyana hadin kai da gwamnati da al'ummar Venezuela, ya sanar da shirye-shiryen ƙasarsa don gudanar da duk wani taimako a ayyukan agaji da ceto.
Baqa'i ya kuma nanata cewa, ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran tun daga farkon sa'o'in da lamarin ya afku, tana tuntuɓar ofishin jakadancin ƙasar a Caracas don samun labaran abubuwan da ke faruwa, kuma ta sanar da shirye-shiryen Iran don taimakawa gwamnatin Venezuela don fuskantar sakamakon wannan girgizar ƙasa mai tsanani.
...........
Your Comment