Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Hedkwatar Khatamal-Anbiya (S.A.W) ta tsakiya ta fitar da wata sanarwa da ke cewa: A ci gaba da munanan ayyukan Amurka mai ta’addanci, bisa la'akari da fara hare-haren sojojin mamaya na wannan ƙasa a wasu yankunan kudancin lardin Hormozgan, daga wannan lokaci saboda rashin tsaro a yankin, an rufe mashigar Hurmuz ga kowane irin jirgin ruwa ko da na dakon mai ne ko na kasuwanci, kuma duk wani yunkurin wucewa za a kai masa hari.
A cikin sanarwar an kara da cewa, ana musanta iƙirarin Amurka game da wucewar jirgin ruwa ta mashigar da aka ambata.
Rundunar sojan ruwa ta dakarun juyin musulunci na Iran ita ma a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa, biyo bayan keta yanayin tsagaita wuta da makiya Amurka suka yi akai-akai, an rufe mashigar Hurmuz har sai an ba da sabon sanarwa.
Wannan sanarwa ta kara da cewa: Muna yin gargadi cewa kada wani jirgin ruwa ya motsa daga tasharsa a cikin Tekun Farisa da tekun Oman. Matsowa kusa da mashigar Hurmuz za a ɗauka a matsayin hadin kai da makiya.
A cikin sanarwar rundunar sojan ruwa ta dakarun juyin musulunci an bayyana cewa, an kai hari kan jiragen ruwa biyu masu bijerewa da suka yi yunkurin wucewa ta mashigar Hurmuz.
Tun daga 'yan sa'o'i da suka gabata, sabon hare-haren Amurka a kan Iran ya fara da kai hari a wasu yankunan da ke gefen tekun kudancin ƙasar.
............................
Your Comment