Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An fitar da bidiyon lokacin da sojojin sahayoniya suka sace wani kwale-kwale na ayarin Samuod
Bidiyon da aka fitar na nuna ɗaya daga cikin kwale-kwalen ayarin Samoud sojojin sahayoniya sun shiga cikin wannan jirgin ruwa da ya doshi karya killacewar Gaza, wanda suka shafe mintuna 40 suna bibiyarsa.
Wannan bidiyon ya nuna wasu mahara na runduna ta 13 ta sojojin ruwan sahayoniya suna shiga jirgin tare sace shi.
Masu shirya Ayarin Samoud ta Duniya sun bayyana cewa jiragen ruwa na soja sun tare hanyar wannan ayarin na ruwa, kuma sun haye kan kwale-kwalen tare da karkatar da shi
Your Comment