18 Mayu 2026 - 20:38
Source: ABNA24
Sojojin Isra'ila Sun Kwace Jiragen Ruwa Ayarin Samoud + Bidiyo

Majiyoyin yahudawa sun bayyana cewa sojojin ruwan Isra'ila sun kama mutane 100 daga cikin fasinjojin ayarin Samoud da ke tafiya daga Turkiyya zuwa Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An fitar da bidiyon lokacin da sojojin sahayoniya suka sace wani kwale-kwale na ayarin Samuod

Bidiyon da aka fitar na nuna ɗaya daga cikin kwale-kwalen ayarin Samoud sojojin sahayoniya sun shiga cikin wannan jirgin ruwa da ya doshi karya killacewar Gaza, wanda suka shafe mintuna 40 suna bibiyarsa.

Wannan bidiyon ya nuna wasu mahara na runduna ta 13 ta sojojin ruwan sahayoniya suna shiga jirgin tare sace shi.

Masu shirya Ayarin Samoud ta Duniya sun bayyana cewa jiragen ruwa na soja sun tare hanyar wannan ayarin na ruwa, kuma sun haye kan kwale-kwalen tare da karkatar da shi

Your Comment

You are replying to: .
captcha