17 Mayu 2026 - 23:45
Source: ABNA24
Hizbullah Ta Raunata Sojojin Isra'ila 105 Da Jirage Marasa Matuki Da Bama-Bamai

Rundunar sojan Isra'ila ta bayyana cewa sojojinta 105 sun samu raunuka a fadace-fadacen da ke kudancin Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Rundunar sojan Isra'ila a yau Lahadi ta sanar cewa sakamakon fashewar wani bam da aka dasa a gefen hanya a kudancin Lebanon, sojojin Isra'ila hudu sun samu raunuka. A cewar rundunar, a cikin makon da ya gabata, sojojin Isra'ila 105 ne suka samu raunuka a fadace-fadacen kudancin Lebanon.

Kamar rahoton tashar Al Jazeera ya ce rundunar sojan Isra'ila a wata sanarwa ta bayyana cewa: A daren jiya, wani sojan Isra'ila ya samu mummunan rauni, sannan wani jami'in soja kuma ya samu matsakaicin rauni; wannan lamarin ya faru ne sakamakon fashewar wani bam a gefen hanya a kudancin Lebanon.

Sanarwar ta kara da cewa: A wannan lamarin, wani jami'in yaki da wani soja sun samu kananan raunuka, kuma an kai wadanda suka jikkata asibiti.

Bayan 'yan sa'o'i, rundunar sojan Isra'ila ta kuma bayyana cewa Hizbullah ta harba jirage marasa matuki da rokoki kan sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon, ba tare da yin tsokaci kan asarar rayuka ko barna ba.

Rundunar sojan Isra'ila kullum tana aiwatar da tsauraran matakan tantancewa da sa ido na soji kan asarar rayuka da barnar dukiya sakamakon yakinta a yankin, tare da iyakance hotuna da bidiyoyin da ke da alaka da wadannan barnar.

Martanin Hizbullah

Hizbullah kuma a ranar Lahadi ta sanar cewa, a matsayin martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Tel Aviv ke yi, ta kai hari kan wata bolidozar da tarin motoci da sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon.

Wannan kungiya a wata sanarwa ta bayyana cewa, ta kai harin manyan rokoki kan taron sojojin Isra'ila a yankin "Khalet Raj" a garin Deir Siryan da ke kudancin Lebanon.

A wata sanarwar kuma, an bayyana cewa dakarun kungiyar sun kai hari kan taron motoci da sojojin Isra'ila a garin Rashaf da ke lardin Nabatiyeh da makamai masu linzami.

Hizbullah a sanarwa ta uku ta kuma bayyana cewa, dakarunta sun kai hari kan wata bolidozar rundunar sojan Isra'ila a garin Al-Bayyada da ke lardin Kudu, inda suka kai harin da jirgi mara matuki na kunar bakin wake, suka kuma same ta.

Kungiyar ta jaddada cewa ayyukanta sun kasance a matsayin martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila take yi, da kuma hare-haren da take kaiwa kauyukan kudancin Lebanon wanda ya janyo kashewa da raunata wasu fararen hular Isra'ila.

Hizbullah a martanin da take ta kaiwa kan Isra'ila bayan take yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kafa tun ranar 17 ga watan Afrilun da ya gabata, ta ci gaba da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki kan sojoji da kayan aikin sojan Isra'ila a kudancin Lebanon da arewacin Isra'ila.

Jirage marasa matuki na Hizbullah, musamman wadanda ake sarrafa su ta hanyar fiber optic, yanzu sun zama babbar barazana ga rundunar sojan Isra'ila; ta yadda kayan aikin ganowa suka zama makamin kai hari, wanda yake da matukar wahala a iya jin gargadin zuwansu ko kuma tunkararsu, kuma Tel Aviv na neman mafita ga wannan batu.

A ranar Alhamis din da ta gabata, an gudanar da zagaye na uku na shawarwari tsakanin Lebanon da Isra'ila a Washington, inda daga karshe aka tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin zuwa wasu kwanaki 45 har zuwa farkon watan Yuli.

Rundunar sojan Isra'ila tun daga ranar 2 ga watan Maris na shekara 2026, ta fara kai hare-hare a Lebanon, wanda bisa kididdigar hukuma, ya kai ga shahadar 'yan kasar Lebanon 2,998 da raunata wasu 9,210, sannan ya raba sama da 'yan Lebanon miliyan daya da muhallansu.

Rundunar sojan Isra'ila tana rike da wasu yankuna a kudancin Lebanon; wasu daga cikin wadannan yankuna tun shekaru da dama da suka gabata take rike da su, wasu kuma tun lokacin yakin shekarun 2023 da 2024. Haka kuma, a cikin hare-haren baya-bayan nan, sojojin Isra'ila sun ci gaba har zuwa kusan kilomita 10 a cikin iyakokin kudancin Lebanon.

Your Comment

You are replying to: .
captcha