10 Mayu 2026 - 23:59
Source: ABNA24
Iran Ta Bayar Da Amsa Kan Bayin Kawo Ƙarshen Yaƙi

Majiyoyin Diflomasiyya sun fitar amsar Iran ga Amurka wacce ta ƙunshi buƙatar kawo ƙarshen Ƙƙawanyar ruwa da ’yancin da fitar da mai.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Amsar da Iran ta aike ta hannun Pakistan a matsayin mai shiga tsakani, tana ƙunshe da wani sashi game da tsagaita wuta a Lebanon.

Sanya batun tsagaita wuta a Lebanon a cikin amsar Iran, yana cikin jajayen layukan da Iran ba za a ƙetara su ba a tattaunawar.

Tehran ta danganta wasu daga cikin yarjejeniyoyin da aka gabatar da wasu lamuran da suka shafi kawo ƙarshen tashin hankali a Lebanon.

Duk wata yarjejeniya da Amurka, dole ne ta ƙunshi kawo ƙarshen yaƙi nan take da zarar an sanar da ita.

Iran ta nanata buƙatar soke takunkumin Amurka da kuma ’yanto da kadarorinta da aka killace.

Tehran na buƙatar soke takunkumin “OFAC” da suka shafi siyar da man Iran.

Amsar Iran ta fayyace cewa ita ce ke da alhakin kula da mashigar Hormuz a cikin yarjejeniyoyin da aka gabatar.

Yarjejeniyar da aka ba da shawarar ta ƙunshi tattaunawar kwanaki 30 bayan tsagaita yaƙi don tattauna cikakkun bayanai.

Iran ta ba da shawarar wasu matakai na gaba-gaba don gwada sahihancin gaskiyar Amurka wajen aiwatar da alkawurran da ta ɗauka.

Tattaunawar tsakanin Tehran da Amurka a yanzu za ta ci gaba ta hanyar musayar rubuce-rubuce da kuma Pakistan a matsayin mai shiga tsakani.

..........................

Your Comment

You are replying to: .
captcha