10 Mayu 2026 - 23:53
Source: ABNA24
Kwamandan Sansanin ‘Hatamul Anbiya’ Ya Gana Da Jagora

Babban Janar Sojan Juyin Juya Halin MusulunciAli Abdullahi, a lokacin da ya kai ziyara ga Mai Girma Babban Kwamandan Sojojin Ƙasar kuma jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i (Allah ya tsare shi), ya mika rahoton halin da Sojojin Ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke ciki, wanda ya hada da Sojojin Jamhuriyar Musulunci, Rundunar Irgc da jami’an Tsaro da ‘Yan Sanda da Masu tsaron iyakokin ƙasar, Ma’aikatar Tsaro, da dakarun Basij.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kwamandan Rundunar ‘Hatamul Anbiya’ a cikin wannan rahoton ya bayyana cewa, dukkan mayaƙan Musulunci suna cikin shiri sosai ta fuskar ruhiyyar yaƙi, shirye-shiryen kai hari da tsaro, dabarun yaƙi, da kayan aiki da makaman da ake buƙata domin fuskantar ayyukan maƙiya Amurka da Sahayoniya. Ya kuma ce idan suka yi wani kuskure na dabara, ko kutsawa ko zalunci, za a tunkare su da gaggawa, da ƙarfi, da tsauri.

Babban Matukin jirgin sama Ali Abdullahi, a madadin dukkan mayaƙan Musulunci da Sojojin Ƙasar, ya ba wa Mai Girma Babban Kwamandan Sojojin Ƙasar tabbacin cewa, tare da cikakken bin umarninsa, za su kare manufofin Juyin Musulunci, ƙasar Iran, ikonta da muradun ƙasa da al’ummar Iran masu kishin ƙasa da jarumtaka, har zuwa ƙarshen rayuwarsu. Za su kuma sa maƙiya mamugunta, maƙiya masu ƙiyayya da zalunci su yi nadamar munanan manufofinsu na yaƙar ƙasar.

A wannan ziyarar, Mai Girma Babban Kwamandan Sojojin Ƙasar, yayin da yake jinjina da godiya ga dukkan jajirtattu mayaƙan da jarumai da kuma Sojojin Ƙasar masu ƙarfi, bayan shirye-shiryen da ya yi a baya a lokacin yakin da aka yi wa Iran a karo na uku, ya ba da sabbin umarni masu buɗe hanya don ci gaba da ayyukan da kuma fuskantar maƙiya cikin ƙarfi.

....................

Your Comment

You are replying to: .
captcha