Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Radiyon sojojin Isra'ila, wanda ke magana game da kwace jiragen ruwa 21 daga cikin jimillar jiragen ruwa 58 na ayarin jiragen ruwan na Al-Samoud da suke tafiya domin kai ɗauki ga al'ummar Falasɗinu, ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a dauki mataki kan sauran jiragen idan ba su canza hanya ba don komawa.
Tashar talabijin ta Isra'ila ta 12 ta kuma ruwaito cewa rundunar sojin ruwan gwamnatin ta sanar da masu fafutukar da ke cikin wadannan jiragen cewa suna cikin kamu da dauri ne.
Your Comment