28 Afirilu 2026 - 11:17
Source: ABNA24
Amurka Na Ci Gaba Da Fashin Teku Ga Man Iran

Jiragen dakon mai na Iran da Amurka ta sace suna ci gaba tafiya zuwa inda ba a sani ba’ Amma ana ta yin hasashe kamar tafiya zuwa Afirka ko ma zuwa yankin sansanin sojin Amurka a Diego Garcia ne.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A wani rahoto Bloomberg ta rubuta cewa jiragen dakon mai guda biyu masu alaka da Iran, wadanda sojojin Amurka suka tsayar a makon da ya gabata kusa da Sri Lanka, yanzu suna tafiya zuwa yammacin tekun Indiya. Amurka ba ta bayar da wani bayani a hukumance game da abin da take son yi da wadannan jiragen dakon mai ba. Amma ana ta yin hasashe kamar tafiya zuwa Afirka ko ma zuwa yankin sansanin sojin Amurka a Diego Garcia ne.

Your Comment

You are replying to: .
captcha