26 Afirilu 2026 - 22:40
Source: ABNA24
Iran Na Ci Gaba Da Fitar Da Manta Zuwa Kasuwa Duk Da Kawanyar Amurka

Bloomberg: Iran na ci gaba da loda man fetur a kan tankunan mai duk da kawanyar da Amurka ta yi a tekun Oman

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wasu jiragen ruwa sun sami nasarar ketare kawanyar Amurka ta hanyar kashe na'urar tsarin bin diddigi ko amfani da hanyoyi marasa tushe; ta yadda jiragen ruwa da dama da ke cike da mai suka bar Tekun Farisa, suna masu dauke da miliyoyin ganga na man Iran zuwa kasuwa. 

Tankers Trackers ta rubuta: Iran ta loda ganga miliyan 4.6 na man fetur a tashoshin man fetur ɗinta. Da alama ganga miliyan huɗu na man Iran sun sake tsallake daga kawanyar sojojin 'yan ta'adda na Amurka.

Your Comment

You are replying to: .
captcha