18 Afirilu 2026 - 23:57
Source: ABNA24
Shekh Naeem: Za Mu Mayar Da Martani Ga Keta Yarjejeniyar Da Isra'ila Ta Yi

Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ya yi gargadi game da ci gaba da ta'addancin Isra'ila tare da sanar da cewa gwagwarmaya za ta mayar da martani ga duk wani keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta kuma dakarunta za su ci gaba da kasancewa a shirye a filin daga.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sheikh Naeem Qasim, Shugaban Hizbullah Labanon, ya jaddada cewa, gwagwarmaya zata mayar da martani ga keta iyakar Isra'ila kan tsagaita bude wuta na wucin gadi. Sannan ya sanar da cewa shirin Hizbullah na yin hadin gwiwa da gwamnatin Lebanon ta hanyar sabon shafi bisa la'akari da tabbatuwar mulkin hukumar wannan kasa.

Ya kara da cewa: "Tsagaita wutar na nufin dakatar da duk wani aikin yaki," Domin ba mu da aminci ga wannan abokin gabar, dakarun gwagwarmaya za su ci gaba da kasancewa a filin daga, hannayensu za su kasance a kan makamansu wanda zai daidai da duk martani ga keta iyaka.

Sakatare Janar na Hizbullah na Lebanon ya kuma jaddada cewa tsagaita wutar ba za ta kasance daga Gwagwarmaya ba kawai, sai dai dole ya zama daga bangarorin biyu su aiwatar da shi. Gwagwarmaya ba za ta amince da maimaita hakurin watanni goma sha biyar ba a yayin da Isra'ila ta kai ci gaba da kai hari a cikin fatan smaun mafutar diflomasiyyar da ba ta da wani sakamako. Ya ce: “Mataki na gaba shi ne a dakatar da ta’addancin da ake yi wa dukkan kasar Lebanon a kan kasa na dindin-dindin ta sama da kasa da teku, da kuma janye sojojin Isra’ila daga yankunan da aka mamaye zuwa kan iyakoki, da sakin fursunoni, da mayar da mutane zuwa kauyukansu da garuruwansu har zuwa kan iyakoki, da kuma fara sake ginawa tare da goyon bayan kasa da kasa da na Larabawa da alhakin hakan ya hau kansu.

Filin Daga Ne Zai Yanke Hukunci.

Sheikh Naeem Qasim ya jaddada a farkon jawabinsa: Filin daga ya tabbatar da cewa shi ne ma’abocin kalmar karshe da siyasa mai nasara’ siyasar da ke amfani da sakamakon filin daga a matsayin tushen iko don tilasta wa makiyiya Isra'ila. Ya kara da cewa: "Ba za a taba cimma tsagaita bude wuta na wucin gadi ba idan ba don jihadin 'yan gwagwarmayar gwagwarmaya a fagen masu daraja na kudancin Lebanon ba." Ya kuma ce Iran ta dage akan tsagaita wuta a yarjejeniyar da ake a Pakistan da ta hada da Lebanon, Wannan batun kuma karara an bayyana shi a fili a cikin wata sanarwa a hukumance, sannan ta rufe mashigar Hurmuz ne a gaban cin keta iyakar da Amurkawa ke yi a Lebanon.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha