18 Afirilu 2026 - 21:53
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Lebanon

Kafofin yada labarai na Hebrew sun ba da rahoton cewa, duk da tsagaita wuta da aka yi a Lebanon, sojojin sahyoniyawa uku sun jikkata a wani lamari kuma an kai su da jirgi mai saukar ungulu zuwa asibitin Rambamah da ke Haifa. Wadannan kafofin watsa labarai ba su ambaci yanayi da cikakkun bayanai na wannan lamarin ba. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labaran kasar Lebanon sun ba da rahoton cewa, sojojin da suke mamaye a sassan kudancin kasar ne suka gudanar da ayyukan ta'addanci da dama. 

Dakarun sahayoniyawan mamaya sun gudanar da ayyukan fashewar wani bom a garin Al-Kiyyam lamarin da ya haifar da arangama da Hizbullah inda aka ga an dauke wasu sojojin sahyoniyawa da suka jikkata a kudancin Lebanon zuwa Haifa. 

Kafofin yada labarai na Hebrew sun ba da rahoton cewa, duk da tsagaita wuta da aka yi a Lebanon, sojojin sahyoniyawa uku sun jikkata a wani lamari kuma an kai su da jirgi mai saukar ungulu zuwa asibitin Rambamah da ke Haifa. Wadannan kafofin watsa labarai ba su ambaci yanayi da cikakkun bayanai na wannan lamarin ba. 

Your Comment

You are replying to: .
captcha