Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rusa kungiyoyin ta'addanci a karkashin jagorancin Amurka da Isra'ila bayan ayyukan da jami'an leken asiri da tsaro a kudu maso gabashin kasar, da dama daga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda na Amurka da gwamnatin Sahayoniyya da ke son gudanar da ayyukan ta'addanci a lokacin hare-haren sama da Amurka da Isra'ila suka gudanar a Iran wanda sun so gudanar da ayyuka irinsu kashe shugabanni da dasa bama-bamai a gefen hanyoyi da kai hari kan wuraren sojoji wanda aka gano su tare da tarwatsa su.
A yayin wannan farmakin, an kama yan ta'adda 55 ya zuwa yanzu kuma an kashe 13 daga cikin su an kama manyan makamai, bama-bamai da na'urorin sadarwa na gwamnatin ta'addancin Amurka.
'Yan ta'addan da aka kama suna da manufar tattara bayanai daga cibiyoyi masu mahimmanci don taka rawar "Mataki Na Biyar Na Yaƙin" don taimakawa wajen hare-haren jiragen saman Amurka, wanda akai maganin hakan da sa ido mayakan Islama.
Your Comment