20 Maris 2026 - 14:14
Source: ABNA24
Iran: Ta Harbo Jirgin Yaƙin Amurka Nau'in F-35 Da Amurka Ke Ji Da Shi

Jami'an tsaron juyin juya hali sun sanar da Harbo Jirgin Yaƙin Amurka Nau'in"F-35"

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ofishin hulda da jama'a na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya sanar da kai hari kan wani jirgin yaƙin Amurka nau'in F-35 na sojojin Amurka a tsakiyar sararin samaniyar Iran, yana mai tabbatar da cewa a harin an yiwa jirgin lahani mai tsananin da ya sanya ya tsere cikin gaggawa. 

Jami'an tsaron juyin juya hali sun ce a cikin wata sanarwa da ya fitar: Da karfe 2:50 na safiyar yau, ta hari wani jirgin F-35 tare da raunata shi jirgin da sojojin Amurka a ƙoƙarin kai hari da shi a tsakiyar sararin samaniyar Iran, an kaiwa jirgin hari ta hanyar sabbin na'urorin tsaro na zamani masu ci na dakarun juyin juya hali, Har yanzu ba a san makomar jirgin ba kuma ana kan bincike, tare da yuwuwar faduwarsa. 

Rahoton ya yi nuni da cewa, bayan nasarar harbo jiragen sama marasa matuki na Amurka da na sahyoniya 125 da tsarin tsaro na Iran suka yi, wannan tsari mai nasara ya nuna gagarumin sauye-sauye a tsarin tsaron saman kasar.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha